Quotes of The Week

Lokaci ya yi da zamu rage jayayya cikin abubuwan da ba zasu Amfanemu ba, mu mayar da Hankali cikin: - Ceto Imani daga Mulhidai - Ceto Hankali daga Miyagun Qwayoyi - Ceto Tarbiyah daga Gurbatattun Al’adu


~ @Profmaqari

Ta’addanci, Jahilci da Quncin Rayuwa; Abokan Gaba ne da ya wajaba a kan dukkan Mutane, Musamman Al’ummar Musulmi, su yi taron dangi wajen gusar dasu


~ @Profmaqari

Ya kamata duk Mai Hankali ya zama yana da tsarin abinda yake son yi a shekarar da zata shigo 2021 Idan abinda Mutum yake son yi ba khidima ga Musulunci da Musulmai ne a farko ba ya kamata ya canza shawara Allah Ya iya mana


~ @Profmaqari

Idan baka zama Na farko ba ka tabbata baka rasa Na biyu ba - Mai Nufin Allah cikin dukkan Lamurransa - Wanda ya sanya Mutuwa a gaban Idonsa


~ @Profmaqari

Today matters, focus on Now!


~ @Profmaqari

Abinda ya Halatta Don Lalura yana gushewa da gushewar Lalurar Lokaci yayi da a kowani Gari a Qasarmu DOLE masu hali su samar da Asibitoci Na Mata zalla wanda duk Ma’aikatansu zasu zama Mata Wannan yana daga cikin Farillan Jama’a wanda Idan ba a yi ba kowa yana da zunubi Allah Ya iya mana


~ @Profmaqari